1 Corinthians 7

Aure

1To, game da zancen da kuka rubuta: Yana da kyau mutum yǎ zauna ba aure.
Ko kuwa “Ya fi kyau kada mutum yǎ yi jimaʼi da mace.”
2Amma da yake fasikanci ya yawaita sosai, ya kamata kowane mutum yǎ kasance da matarsa, kowace mace kuma da mijinta. 3Ya kamata miji yǎ cika hakkinsa na aure ga matarsa. Haka kuma matar ta yi ga mijinta. 4Jikin matar ba nata ne kaɗai ba, amma na mijinta ne ma. Haka ma jikin mijin, ba na shi ne kaɗai ba, amma na matarsa ne ma. 5Kada ku ƙi kwana da juna sai ko kun yarda a junanku kuma na ɗan lokaci, don ku himmantu ga adduʼa. Saʼan nan ku sāke haɗuwa don kada Shaiɗan yǎ jarabce ku saboda rashin kamewarku. 6Wannan fa shawara ce nake ba ku, ba umarni ba. 7Da ma a ce dukan maza kamar ni suke mana. Sai dai kowa da irin baiwar da Allah ya yi masa; wani yana da wannan baiwa, wani kuwa wancan.

8To, ga marasa aure da gwauraye kuwa ina cewa: Yana da kyau su zauna haka ba aure, yadda nake. 9Sai dai in ba za su iya kame kansu ba, to, su yi aure, don ya fi kyau a yi aure, da shaʼawa ta sha kan mutum.

10Ga waɗanda suke da aure kuwa ina ba da wannan umarni (ba ni ba, amma Ubangiji) cewa: Kada mace ta rabu da mijinta. 11In kuwa ta rabu da shi, sai ta kasance ba aure, ko kuma ta sāke shiryawa da mijinta. Kada miji kuma yǎ saki matarsa.

12Ga sauran kuwa (ni ne fa, ba Ubangiji ba) na ce: In wani ɗanʼuwa yana da mata wadda ba mai bi ba ce, kuma tana so ta zauna tare da shi, kada yǎ sake ta. 13In kuma mace tana da miji wanda ba mai bi ba ne, kuma yana so yǎ zauna tare da ita, kada ta kashe auren. 14Don miji marar ba da gaskiya an tsarkake shi ta wurin matarsa. Mace marar ba da gaskiya kuma an tsarkake ta ta wurin mijinta. In ba haka ba ʼyaʼyanku ba za zama da tsarki ba, amma kamar yadda yake, su masu tsarki ne.

15Amma in marar bi ɗin ya raba auren, a ƙyale shi. A irin wannan hali, babu tilas a kan wani, ko wata mai bi. Allah ya kira mu ga zaman lafiya ne. 16Ke mace, kin sani ne, ko ke ce za ki ceci mijinki? Kai miji, ka sani ne, ko kai ne za ka ceci matarka?

17Duk da haka, sai kowa yǎ kasance a rayuwar da Ubangiji ya sa shi da kuma wanda Allah ya kira shi. Umarnin da na kafa a dukan ikkilisiyoyi ke nan. 18In an riga an yi wa mutum kaciya saʼad da aka kira shi, to, kada yǎ zama marar kaciya. In an kira mutum saʼad da yake marar kaciya, to, kada a yi masa kaciya. 19Kaciya ba wani abu ba ne, rashin kaciya kuma ba wani abu ba ne. Kiyaye umarnin Allah shi ne muhimmin abu. 20Ya kamata kowa yǎ kasance a matsayin da yake ciki saʼad da Allah ya kira shi. 21Kai bawa ne saʼad da aka kira ka? Kada wannan yǎ dame ka-sai dai in kana iya samun ʼyanci, sai ka yi amfani da wannan dama. 22Gama wanda yake bawa saʼad da Ubangiji ya kira shi, ʼyantacce ne na Ubangiji; haka ma, wanda yake ʼyantacce saʼad da aka kira shi, bawa ne na Kiristi. 23Da tsada fa aka saye ku, kada ku zama bayin mutane. 24ʼYanʼuwa, a duk matsayin da mutum yake saʼad da aka kira shi, sai yǎ kasance haka a sabuwar dangantakarsa da Allah.

25To, game da budurwai: Ba ni da wani umarni daga Ubangiji, sai dai na yanke hukunci a matsayi wanda yake amintacce ta wurin jinƙan Ubangiji. 26Saboda ƙuncin rayuwar da ake ciki, ina gani ya fi kyau ku kasance yadda kuke. 27In kuna da aure, kada ku nemi kashe auren. In ba ku da aure, kada ku nemi yin aure. 28Amma idan ka riga ka yi aure, to, ba laifi, ba zunubi ba ne, kuma idan yarinya
yarinya: Da Helenanci an rubuta “budurwa” ne nan.
ta yi aure, ba ta yi laifi ba. Sai dai waɗanda suka yi aure za su fuskanci damuwoyi masu yawa a cikin rayuwa, ni kuwa ina so in fisshe su daga wannan.

29ʼYanʼuwa, abin da nake nufi shi ne, lokaci ya rage kaɗan. Daga yanzu, waɗanda suke da mata ya kamata su yi rayuwa kamar ba su da su; 30waɗanda suke kuka kuma kamar ba kuka suke yi ba, waɗanda suke farin ciki kuwa kamar ba farin ciki suke yi ba. Waɗanda suka sayi abu su yi kamar ba nasu ba ne; 31masu amfani da kayan duniya kuwa, kada su duƙufa a cikinsu. Gama duniyan nan a yadda take mai shuɗewa ce.

32Zan so ku ʼyantu daga damuwa. Mutum marar aure ya damu ne da alʼamuran Ubangiji-yadda zai gamshi Ubangiji. 33Amma mutumin da yake da aure yakan damu ne da alʼamuran wannan duniya-yadda zai gamshi matarsa—  34hankalinsa a rabe yake. Mace marar aure ko kuwa budurwa ta damu ne da alʼamuran Ubangiji: Nufinta shi ne ta ba da kanta ga Ubangiji cikin jiki da ruhu. Amma mace da take da aure ta damu ne da alʼamuran wannan duniya-yadda za ta gamshi mijinta. 35Na faɗa haka don amfaninku ne, ba don in ƙuntata muku ba. Sai dai don ku yi rayuwa a hanyar da ta dace da nufin ku himmantu ga bautar Ubangiji ba da raba hankali ba.

36In mutum ya ga cewa ba ya nuna halin da ya kamata ga budurwar da ya yi alkawarin aure da ita, in kuma shekarunta suna wucewa, shi kuma ya ga ya kamata yǎ yi aure, to, sai yǎ yi. Ba zunubi ba ne. Ya kamata su yi aure. 37Amma mutumin da ya riga ya yanke shawara a ransa, wanda kuma ba lalle ba ne amma yana iya shan kan nufinsa, kuma ya riga ya zartar a zuciyarsa ba zai auri budurwar ba—wannan mutum ma ya yi abin da ya dace. 38Don haka, wanda ya auri budurwar ya yi daidai, amma wanda bai aure ta ba ya ma fi.
Ko kuwa 36 In wani yana tsammani cewa ba ya yin wa ʼyarsa abin da ya dace, in kuma shekarunta suna karuwa, ya kuwa ji ya kamata ta yi aure, sai yǎ yi yadda ya ga ya dace. Bai yi zunubi ba. Ya kamata yǎ bar ta ta yi aure. 37 Amma mutumin da ya warware batun a zuciyarsa, wanda ba ya ƙarƙashin tilas amma yana iya sarrafa nufinsa, wanda kuma ya yanke shawara yǎ bar budurwarsa ba aure-wannan mutum ma ya yi abin da yake daidai. 38 Saboda haka, wanda ya ba da budurwarsa a aure ya yi daidai, amma wanda bai ba da ita ga aure ba ya ma yi abin da ya fi.


39Mace tana haɗe da mijinta muddin yana da rai. Amma in mijinta ya mutu, tana da ʼyanci ta auri wanda take so. Amma fa, sai mai bin Ubangiji. 40A nawa raʼayi, za ta fi jin daɗi in ta zauna haka-a ganina kuwa ina ba ku shawara ce daga Ruhun Allah da na ce haka.

Copyright information for HauSRK